wanna shafi yana zuwa muku kai tsaye daga masallacin jumu'a Jami'u Abu hurairah Dake kurna y'an kifi titin y'an smogal a karamar hukumar dala dake kano Nigeria kar kashin jagorancin Sheik Muhammad Sani Uthman Kurna
----------------------------------- FALALAR KARATUN AL QUR`ANI
KASHI NA UKU 3
SAKAMAKON.WANDA YARONSA YA KOYI KARATUN AL QUR`ANI
MANZON ALLAH SAW YA CE"wanda ya karanci al qur`ani kuma ua san shi ya kuma yi aiki.da shi za a sanyawa iyayensa,biyu hular girma ta haske ranar tashin kiyama,hasken hular kamar hasken rana ne,kuma za a tufatar da iyayensa guda biyu tifafin kwalliya wnda duniya bata kai su daraja ba.dai iyayen guda biyu su ce "dan me aka tufatar da mu wannan kayan?" Sai ace musu "saboda rukun da danku yAyi al qurani,(Hakim).
CETON AL QUR'ANI GA MA'ABOCINSA(MAHADDACINSA)A LAHIRA
MANZON ALLAH S.A.W YA CE"KU KARANTA AL QUR'ANI SABODA ZAI ZO RANAR TASHIN ALKIYAMA YANA MAI CETO GA MA'ABOTANSA" (muslaim).
MANZAON ALLAH S.A.W YA KARA CEWA"AZUMI DA ALQUR'ANI ZASU CETO GA BAWA RANAR TASHIN ALKIYAMA"(Ahmad da Hakim).
LADAN HADUWA KAN TILAWAR ALQUR'ANI DA YIN DARASI A CIKINSA
MANZON ALLAH S.A.W YACE "MUTANE BASU TABA HADUWA BA, A CILIN WANI GIDA DAGA CIKIN GIDAJEN ALLAH(MASALLACI)SUNA KARANTA LATTAFIN ALLAH KUMA SUNA KOYAR DA SHI A TSAKANINSU,FACE SAI NUTSUW TA SAUKA A GARE SU,KUMA RAHAMA TA LULLUBE SU,KUMA MALAIKU SU KEWAYESU,SANNAN KUMA ALLAH YA AMBA CE SU GA WADANDA SUKE WAJENSA WATO (MALAIKU). (Abu dawud)
WASU DAGA HUKUNCE HUKUNCEN KARATU
LADDUBAN KARATUN AL QUR'ANI
IBN KHASIR ya ambaci wani sashi daga cikin ladduban kamar haka yace"kada mutum ya shafi alqur,ani kuma kada ya karantashi face yana tsarki,kuma sannan yayi asuwaki kafin fara karatunshi,kuma ya sanya mafi kyawu daga cikin tufafinsa,kuma ya fuskanci alqibla,ya tsayar da karatunsa yayin himma,kada ya yanke karatunsa domin ko yayin wata magana sai inda bukatar hakan ya halarto da hakalunsa yayin karatun ya tsaya akan kowacce aya,da aka yi magana akan rahama domin ya roki ALLAH wannnan ni,ima,da kuma tsaya akan ayar azaba domin ya nemi tsari akai,kar ya ajiye alqur,ani a warwatse,kar kuma ya dora wani abu akansa,kada kuma wasu sashi na makaranta su daga murya akan karatun wasu sashin,saboda kada a sami rudani kuma kada a karanta shi a kasuwa da wuraren da ake ihu da wasanni.
YADDA AKE KARANTA AL QUR,ANI
An tambayi Anas dan malik r.a kan yadda karatun ANNABI S.A.W yake,sai ya ce
"Ya kasance yana jan maddah idan ya karanta BISSIMILLIHIRRAHMANIRRAHIM yakan yi maddah akan sunan ALLAH kuma ya kan yi maddah akan rahman kuma ya kan yi maddah akan rahim(bukhari).
RIBANYA SAKAMAKON KARATU
Dukkan wanda ya karanta don ALLAH to za,a bashi lada kuma lallai ana rubanya wannan ladan kuma ana girmamashi a lokacin da zuciyarsa take halarce,kuma yana bibiya da kokarin fahimtar abin yake karantawa,sai ya zama a kowanne harafi ana bashi lada goma 10 har e zuwa ninki dari bakwi 700.
GWARGWADON ABUN DA YA KAMATA A KARANTA A KOWNNE YINI DA DARE NA AL QUR,ANI.
SAHABBAN(R.A) MA,AIKI S.A.W sun kasance su na sanyawa kawunansu wani kaso daga cikin alqur,ani a kowacce rana,sukan dauwama akan kokarin karanta shi,duk a cikin kena bakwai 7,a,a ha hani yazo akan rashin karanta shi a cikin kwana uku 3,ka yi kwadayi ya dan,uwa wjen tafuyar da lokacinka cikin karatun alqur,ani kasanyawa kanka wani abu daga cikin alqur,ani a kowanne yini,ba zaja bar shi ba ya wuce duk yadda abubuwa suka cabe maka,domin masu iya magana sunce"kadan din da ake yi kullum yafi alheri,fiye da mai yawan da ake yi a gutsutstsure,idan ka manta ko kayi barci baka karanta shi ba,to gobe sai ka rama shi,saboda
MANZON ALLAH S.A.W YACE"WANDA YAYI BARCI AKAN KASON DA YAKE KARANTAWA NA DARE,BAI YI BA KO WANI ABU DAGA CIKINSA,SAI YA KARANTA SHI A TSAKANIN SALLAR ASUBAH KO KUMA SALLAR AZUHUR,TO ZA,A RUBUTA MASA LADA KAMAR YA KARANTA SHI A CIKIN DARE".(muslim)
YA DAN'UWA
Kar ka zama daga cikin wadanda suka kauracewa al qur,ani ko suka manta da shi daga cikin kowanne irin nau,i na kauracewa,kamar nisantar karantashi ko kuma kokarin fahaimtarsa ko kuma kokarin aiki da shi ko kum kokarin neman waraka da shi.
Daga naku ABDULMAJID IBN NUHUFALALAR KARATUN ALKUR,ANI
( kashi na biyu) (2)
FALALAR KOYON KARATUN ALKU,ANI DA HADDACE SHI DA. KUMA GWANANCEWA WAJEN IYA KARANTA SHI
manzon Allah. (S a.w) ya ce . Misalin mutimin da yake. Karatun. Alkur,ani. Alhali yana mai kiyaye shi (hardace shi) to yana tare da mala, iku masu girma, tsarkaka kuma misalin wanda ya ke karanta shi alhalin yana mai kai komo da shi sa,annan yana mai tsananin wahala a kansa, to yana da sakamako kashi biyu(sakamakon wahalar da kuma karatun ) ( Bukhari da muslim) (Abin da ake nufi da safaratu a cikin. Hadisin su ne mala ,iku.)
Manzon Allah.( S.a.w) yakara cewa.
Ana.cewa ga maabocin Alkur,ani ( wato. ga mahaddacinsai a alkiyama ) karantaa kuma kayi sama. Ka kuma karanta. Kamar yadda ka kasance ka ke karantawa a duniya lallai matsayinka zai tsaya ne a karshen ayar da ka karanta ta. (Turmizi)
ALKHADDABI-ALLAH YA MASA. RAHAMA YACE
Ya zo a cikin maganganun magabata lallai cewa gwargwadon yawan a yoyin Alkur,ani shi ne gwargwadon matsayi agidan Aljanna. Sai a ce wa mai karatun Alkur,ani ka yi sama gwargwadon abin da ka kasance kana karantanwa (haddacewa) na ayoyin Alkur,ani duk wanda yakaranta. Alkur,. dukkansa to shi zai samu mafi. girman daraja a gidan aljanna a. Ranar lahira wanda kuma ya karanta juzu,i daya daga cikinsa darajarsa za ta kasance gwargwadon abin daya karanta. Sai ya zama gwargwadon ladanka gwargwadon inda karatun ya tsaya.
`.............``.............. .................................. ................................................................................... muhadu a kashi na gabaFALALAR KARATUN ALKUR,ANI
Dukkan yabo ya tabbata ga ALLAH kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga shugbanmu manzon Allah da kuma Alayensa da sahabbansa amma bayan haka lallai Alkur'ani zancan Allah ne kuma falalarsa akan sauran maganganu kamar daukakar Allah ne akan halittunsa karana shi kuwa shi ne abin dayafi falala kan dukkan abin da harshe ke motsi da shi.
KOYON KARATUN ALQUR,ANI DA KOYAR DA SHI DA KARATAR DA SHI YANA DA FALALA MAI YA WA: daga ciki
SAKAMAKON KOYAR DA SHI: Manzon Allah(s.a.w) ya ce mafi alhernku shi ne wanda ya koyi Alqur'ani kuma ya koyar da shi.(bukhari)
SAKAMAKON KARANTA SHI : Manzon Allah (s.a.w) ya ce duk wanda ya karanta harafi daya daga cikin littafin Allah yana da ladan wannan harafi kuma shi ladan za a ninka shi sau goma (turmizi)